Kofar kola Birnin kebbi: Yadda wata Yarinya ta mutu bayan ta taka wayar lantarki | isyaku.com

A ranar Laraba 17 ga Mayu,Wata yarinya mai suna Fadilatu Umaru ta rasa ranta a yayin da ta taka wayar wutan lantarki a wurin aikin wani mai walda a yayin da take wucewa a unguwar Kofar Kola a cin garin Birnin kebbi.ISYAKU.COM ya isa inda lamarin ya faru wanda yake dan tazara ne kadan daga gidan Mahaifin yarinyar inda muka sami Mahaifinta da sauran jama'a ana karbar gaisuwa.

Mahaifin yarinyar mai suna Alh.Umaru Dattiya ya shaida mana cewa "gaskiya ne wannan lamarin ya auku,yace yaran sun fito ne zasu ketara wurin da yake akan titi ne sai suka raba a jikin kwalbati,kafin su wuce mai waldan yana yin walda wa wani vespa keke napep kuma su yaran basu kula da wayoyin wutan ba  karfe wanda 'yan waldan ke makalawa a jikin karfen mota ya fado mata a kafa kuma tana take da daya wayan wutan wanda yayi sanadin makalewarta a wajen wanda daga karshe rai yayi halinsa".

Alh.Umaru ya kara da cewa basu sanar da hukuma ba,"ni ina kusa da gurin amma ban san abin da ke faruwa ba har sai bayan da abin ya faru sai suka dauke ta suka kaita Asibiti,lokacin da na isa Asibiti na sami Likita yana auna ta wanda daga bisani ya shaida mana cewa Allah ya karbi rayuwar Fadila.

Tuni dai aka bizine ta kamar yadda Musulunci ya tanada,Alh.Umaru ya ce baya da wani mataki da yake shirin dauka illa ya bar komi ga Allah saboda komi mukaddari ne".


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN