• Labaran yau

  An tsinci wata gawa a wajen garin Birnin kebbi | isyaku.com

  Wani labari da ke yawatawa a garin Birnin kebbi ya nuna cewa an tsinci wata gawa a wajen garin na Birnin kebbi wanda ba'a san ko waye gawar ba haka kuma ba'a san sanadin mutuwarsa ba.

  Bayanai sun nuna cewa mahukunta a garin na Birnin kebbi sun adana gawar a dakin ajiye gawa ta Asibitin tunawa da Sir Yahaya.

  Majiyar mu ta labarta mana cewa akwai yiwuwar cewa mahukunta a garin na Birnin kebbi zasu nemi izinin Kotu domin a bizine gawar ranar Juma'a idan ba'a sami wanda ya sanshi ko ya san 'yan uwanshi ba.

  ISYAKU.COM ya tuntubi kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Kebbi game da lamarin ta wayan salula amma yunkurin muji ta bakin sa ya ci tura,haka kuma sako ta sms da muka tura bamu sami amsa ba har izuwa lokacin da muka rubuta wannan rahotu.
  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: An tsinci wata gawa a wajen garin Birnin kebbi | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama