Sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha
alwashin maido da kimar kasar a idon duniya, wadda ke fuskantar
baranazar gushewa a baya.
Macron
mai shekaru 39, ya yi alkawarin ne a lokacin bikin rantsar da shi a
matsayin sabon shugaban kasar ta Faransa, da ya gudana yau Lahadi a
birnin Paris, sati guda bayan nasarar da yayi kan Marine Le Pen, a zaben
shugabancin kasar zagaye na biyu a ranar 7 ga watan da muke ciki, da
kashi 65 na kuri’un da aka kada.Daga cikin manyan batutuwan da
Macron yace gwamnatinsa zata fi bai wa muhimmanci akwai sabunta tsare
tsaren tafiyar da fannin tsaron kasar, yin garambawul a fannin kwadago,
sai kuma jagorantar sake saita ginshikan da suka kafa kungiyar tarayyar
turai EU.Macron da ya kuma yi alwashin daukaka ‘yancin Faransawa da dimokaradiyyar kasar, ya zama shugaban kasa mafi karancin Shekaru a tarihin kasar tun bayan Napoleon Bonoparte.
A gobe Litinin ake sa ran sabon shugaba Macron, ya bayyana sunan Firaministan da zasu yi aiki tare, kafin ziyara ta farko bayan rantsar da shi, da zai kai wa shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel a birnin Berlin.
Ana sa ran batutuwan da suka hada da, karfafa turakun da suka kafa kungiyar tarayyar turai EU, da kuma fannin tsaro su mamaye tattaunawar da shugabannin biyu zasu yi.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
Wannan labarin ya fara baiyana a shafin RFI
Tags:
DUNIYA