Birnin kebbi: Yadda Mamuda ya rasa ransa a kan hanyar Gwadangaji | isyaku.com

Mamuda Muhammad dan kimanin shekara 25 wanda ke zaune da iyayensa a unguwar Sarakuna a cikin garin Birnin kebbi sananne a aikinsa na gyaran firjin da na'urar sanyaya daki watau AC yaro ne da aka shaida shi  da hakuri,kunya,girmama na gaba da shi da tsare ibada,kwasam ba zato ba tsammani Mamuda ya yi wafati,ya rasu ne a sakamakon wani hatsari da ya rutsa da shi tsakanin Gwadangaji zuwa Birnin kebbi a yayin da yake dawowa daga wajen aiki a rukunin gidaje na Aliero dake garin Gwadangaji bayan ya afka wa wata tarikita da aka ajiye a gefen titi bayan ta lalace.

Majiyar mu ta labarta mana cewa hatsarin ya faru ne a daidai kusa da Zinari Hotel da misalin karfe tara na dare inda aka  garzaya Asibitin Sir Yahaya da shi wanda aka tabbatar da rasuwarsa bayan aune-aune da Likita yayi.Hatsarin ya faru ne ranar 21/5/2017.

An bizine Mahmuda ranar Talata da misalin karfe 9:00 na safe bayan an gabatar da Sallar Jana'iza.Marigayin ya rasu ya bar Mahaifinsa Alh.Muhammad Na Mandara da Mahaifiyarsa sai yayansa Dauda da sauran kannai.Allah ya karbi bakoncin Mamuda ya kai rahama a kushewarsa da na dukkanin Musulmi ya sa muyi kyakkyawar karshe.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Kana sha'awar ka taimaka mana da labarai daga garin da kake domin mu wallafa a ISYAKU.COM? Ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com ko ka aiko sakon SMS kawai zuwa 08062543120

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN