"Ya kai gafalallen Mutum": Huduba daga Limamin babban Masallacin jihar Kebbi (kaso na 1) | isyaku.comHUDUBAR JUMU'A, MAl TAKEN "YA KAI

GAFALALLEN MUTUM" DA AKA GABATAR A BABBAN MASALLACIN JIHAR KEBBI,

BIRNIN-KEBBI

4-11-2016    4—Safar-1438

Yabo ya tabbata ga Allah da Ya halicci mutum, Ya shiryar da shi zuwa ga Alheri, Ya gargade shi daga sharri, kuma saboda haka ne Ya aiko Manzanni, Ya saukar da littafai. Sai Ya yi bushara, Ya yi gargadi, don a saka wa kowane rai da abin da ya aikata, Allah Marinjayi ne Mai hikima. Allah Shi yi salatida sallama ga Manzonsa da ya zo domin ya fitar da mutane daga duhu zuwa ga hãske da iznin Ubangijinsa Marinjayi Abin Yabo.Bayan haka, Ya kai mutum me ke rudin ka daga Ubangijinka Mai girma, wannan da Ya halicce ka, Ya daidaita ka, Ya kirntsa ka. A cikin kowace siffa Ya so Ya gina ka a kanta, sai ya gina ka. Saboda me kake shagaltuwa daga Ubangijinka sosai? Ka ce dai ba ka ji labarin Manzannin Allah ba, ka ce an bar ka sagaga don ka yl abin da ka ga dama. Hakika ka isa wawa rudadde. Har  zuwa yaushe za ka farka ka yi riko da shiriya? Ko sal mutuwa ta zo maka ka yi nadama lokacih da nadamarka ba- ta da amfani?. Ya kai mutum saboda me kake rayuwa kamar wanda ba ya da Mahalicci Mai iko a kansa? Kana rayuwa jahili gafalalle, alhali Allah Madaukaki na cewa: "Ko mutum na jin cewa a bar shi sagaga?" Kiyama 36.Hakika ka zo Duniya saboda babbar manufa, ita ce bautar Allah da ke cewa: "Ban halicci Aljani da Mutum ba sai don su bauta mini" Ya kuma ce:- 

Wannan da Ya halicci rayuwa da mutuwa don ya jaraba ku (Ya ga) waye a cikin ku ya fi kyawon aiki. Mulku 2. Kuma ka zo Duniya domin ka dauki amanar da Allah ya aza wa bayin Sa, don gyaran rayuwa da gina ta gini kyakkyawa, don samar da al’umma mai bautar Allah, da ba ta hada wani abu da shi, ta kuma samar da jagoranci  shiryaye da ke jagora zuwa ga rabbantar Duniya da lahira. Game da wadannan mutane Allah Madaukaki ke cewa:- "Wadanda in muka ba su iko a cikin kasa, suna tsayar da Sallah, su bada Zakka, su yi umurni da

kyakkyawa aiki su yi hani daga mummuna”  Hajji 41 Ya kuma ce "Wadannan da ba su nunin daukakaa cikin kasa ko barna kuma karshen kwarai na masu tsoron Allah ne". Kasasu 83.Sai day a kai kana almubazzaranci da rayuwarka, ta hanyar dora ta a kan jahilci da gafala da sabo, kila kowane in, kana bata makomarka a Duniyan nan kuma a Lahira ga azaba mai radadi. Sau da yawa kana almubazzaranci ga kanka, sai kana saba wa Allah da sunan neman abinci da neman jin dadi, aihali Allah Madaukaki na cewa:- "Ko mu ba ku labarin masu hasara ga ayukka? Su ne wadanda kokahnsu ya bace a rayu war ..duniya kuma su, suna jin suna kyautata aiki ne. Kahaf 104.Ka manta cewa Mahaliccinka Ya halicce ka ba da izinin ka ko shawararka ko wata isa taka ba? Haka ma da ya sanya karnutum daidaitacce, haka ma da Ya yi ka namiji ko mace. Kuma ba da shawarar ka ko roko daga gare ka ko wata isa taka ba, Ya sanya maka ji, gani, zuciya da hankali.

Zamu ci gaba a kashi na 2.Mun rarraba hudubar saboda tsawon sa.
 
Kana sha'awar ka taimaka mana da labarai daga garin da kake domin mu wallafa a ISYAKU.COM? Ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com ko ka aiko sakon SMS kawai zuwa 08062543120

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN