• Labaran yau

  Ana gudanar da taron sirri tare da manyan jami'an tsaro a fadar shugaban kasa

  A yanzu haka ana gudanar da wani taron sirri a fadar shugaban kasa,majiyar mu ta labarta mana cewa ba'a san abin da ake tattaunawa akai ba.

  Taron yana gudana ne karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ke tafiyar da sha'anin mulkin kasar tun bayan da shugaba Buhari ya tafi London domin tuntuban likitocin sa.

  Cikin wadanda suke a zauren taron yanzu haka sun hada da shugaban Sojin Najeriya  Gebriel Olanishakin (CDS)  da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro Babagana Munguno (NSA),sai kuma Ministan tsaro Mansur Dan-Ali da Ministan zirga-zirga Rotimi Amaechi.

  An fara taron ne da misalin karfe 3:30 kuma ana ci gaba da gudanar da tattaunawar har zuwa wannan lokacin da muka rubuta wannan labarin.

  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Ana gudanar da taron sirri tare da manyan jami'an tsaro a fadar shugaban kasa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama