'Yan sanda sun damke Sule Lamido a Kano

Wani labari ya bayyana cewa hukumar 'yan sandan jihar Kano ta kama tsohon Gwamnan jihar Jigawa Alh.Sule Lamido akan zargin yin katsalandan a zaben kananan hukumomin da ake gudanarwa a cikin jihar ta Jigawa ta hanyar zuga magoya bayansa su kawo cikas a zaben.

Sule Lamido ya jagoranci jihar Jigawa daga 2007 zuwa 2011.Yan sandan sun kama Lamido a gidansa da ke Sharada da safiyar yau inda suka tafi da shi shiya ta daya ta rundunar 'yan sanda da ke Kano inda ake ci gaba da yi masa tambayoyi.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN