Me ya samu Shugaban Nigeria Buhari?

'Yan Nigeria sun yi lale marhabin matuka da dawowar Muhammadu Buhari kan mulki karo na biyu shekara daya da rabi da ta wuce tare da saka fata mai yawan gaske a kansa.
Kusan hankalin kowa ya kwanta lokacin da ya karbi ragwamar mulki daga tsohon Shugaba Goodluck Jonathan - wanda ake yi wa kallon maras katabus.
Sai dai watanni 18 bayan haka, sai ga shi 'yan kasar da yawa na tababar ko sabon shugaban nasu mai shekara 73 na iya shugabantar kasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka, ta yin la'akari da girman matsalolin da take fuskanta yanzu.

 A yayin da ake jinjina wa shugaban kan kokarin da yake na yaki da cin hanci da karbar rashawa da kuma yadda yanzu sojojin kasar ke samun galaba wajen yakin da kungiyar Boko Haram, a wasu fannonin rayuwa ba wani abin a-zo-a-gani.'Yan Nigeria sun yi lale marhabin matuka da dawowar Muhammadu Buhari kan mulki karo na biyu shekara daya da rabi da ta wuce tare da saka fata mai yawan gaske a kansa.
Shugaban Buhari dai ya fada da bakinsa cewa bai shigo da kafar dama ba saboda ya karbi mulkin ne lokacin da farashin danyen mai wanda kasar ta dogara kansa ya fadi kasa warwas


Shugabannin da suka gabata musamman Mista Jonathan, ba su yi tsimin komai ba daga rarar kudaden da kasar ta samu lokacin da farashin gangar mai ke sama ga dala 100 domin irin wannan lokacin da farashin ya fado zuwa dala 30 kacal.
Bugu da kari kuma wawasar kudaden gwamnati ba-kai-ba-gindi ta hana kasar ajiye komai daga cikin kudaden da ta samu ta wasu kafofin.
Kuma hatta kudaden da aka ware domin yaki da Boko Haram wasu daidaikun mutane sun karkata su zuwa amfanin kansu da kuma wajen yakin neman zabe.
Buhari ya amsa cewa ya ji kamar ya gudu ya bar mulki bayan da ya ga yadda girman matsalar take lokacin da ya karbi mulki a watan Mayun shekara ta 2015.

Daga cikin masu sukarsa har da matarsa, wadda ta yi wani abu da ba a saba gani ba, na fitowa ta soki salon shugabancinsa a bainar jama'a a cikin wata hira da BBC.
Inda ta ce ba za ta goyi bayansa ba idan ya ce zai sake tsayawa takara a shekara ta 2019, idan bai sauya salon mulkinsa ba.
Shi ma dai tsohon Shugaban kasar Olusegun Obasanjo, wanda ya ba shi goyon baya lokacin zabe, ya fito fili ya nuna adawa da wasu manufofin gwamnatinsa daga bisani musamman batun karbo bashi na dala biliyan 30.
''Idan ba mu gyara tsarin tattalin arziki ta yadda zai ragewa yawancin 'yan Najeriya wahalhalun da suke ciki ba, nasarar da aka samu wajen yaki da ta'addanci da kuma cin hanci da rashawa za ta zama maras amfani,'' in ji shi.
Da ma ta bangaren tattalin arzikin ne aka fi nuna rashin gamsuwa saboda karayar arzikin da kasar ta fada a yanzu.

Karya darajar kudin kasar Naira, da hauhawar farashin kayan abinci da kuma rasa ayyuka sun jefa iyalai da yawa cikin kunci. Sai da kyar ne wasu ke samu su ci abinci sau daya a rana.
Wannan ne ya sa a kwanan nan 'yan kasar na wasu maganganu na yanke kauna ga shugaban a shafukan sada zumunta irin wannan:
''Yanzu ba so muke Shugaba Buhari ya ciyar da Najeria gaba ba. Muna so ne ya mayar da ita a yadda take kafin ya zamo shugaban kasa.''

A halin da ake ciki yanzu dai yawancin 'yan Najeriya na fatan shugaban da mukarrabansa za su hada karfi wuri daya su fitar da kasar daga karayar arziki mafi muni tun bayan komawar ta kan tsarin dimokradiyya a shekarar 1999 - kana su nuna cewa zabensa ba kuskure ba ne.

Daga BBCHausa, Disamba 9, 2016

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN