Maciji ya kashe wani mutum a yayin da yake daukan hoto da shi

Wani mutum mai suna Baburam dan shekara 42 ya gamu da ajalin sa a yayin da yake kokarin daukan hoto da wani maciji da wani mai wasa da maciji mai suna Indraram Sathur dan shekara 34 ya kawo a kasar Indiya.

Mai wasa da macijin yayi kokarin sanya macijin domin ya zagayo ta wuyar Baburam,amma sai bakin macijin ya kai har gefen goshin Baburam kuma ya sare shi cikin ruwan sanyi ba tare da nuna wani alamar fada ba.

Alamu sun fara bayyana ne a lokacin da Baburam ya koka akan samun damuwa sanadin jini da ke fitowa a gefen goshinsa wajen da macijin ya sare shi.

Sathur mai wasa da maciji yayi kokari domin yayi wa Baburam magani bayan ya dauke shi zuwa wani wajen bauta na addinin Hindu.Bayan awa biyu da bayar da magani kuma babu alamar samun sauki,'yan uwan Baburam sun garzaya da shi zuwa wani Asibiti inda aka tabbatar da mutuwar shi.

'Yan sandan lardin sun kama mai wasa da macijin.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN