Guba da aka sanya wa Buhari,Kuskuren farko Laifin waye? (2)Kamar yadda muka yi bayani a baya,alokacin da jami’an NAIC suka kama aikin tsaron lafiyar shugaba Buhari tare da hadin gwuiwan jami’an DSS wanda aikin su ne a bisa asali da ka’ida su tsare lafiyar shugaban kasa,hakan ya haifar da gibi na rashin yarda da kuma iya fahimtar me kake nufi ko kuma me zaka yi.Saboda kowa yana yiwa dan uwansa kallon kallo.

Marmakin a mayarda hankali wajen kare lafiyar shugaban kasa a bisa akida da tsarin mulki ya shimfida sai aka dawo ana nuna takama da karfin iko,ta hanyar nuna ko ni nafika ko kai baka isa ba domin hurumi na ne tun asali.A bisa nazari na ka’idodin tsaron lafiyar shugaba,wannan wani kuskure ne da zai iya haifar da gibi da makiya zasu samu saboda su cutar da shugaban kasa.

Wasu daga cikin wasu jami’ai da suka shigo cikin jerin masu tsaron lafiyar shugaban kasa,bincike da muka gudanar ya nuna cewa basu sami horo irin wanda ake bayarwa ba don tsaron lafiyar shugaban kasa.A bisa wannan dalili ne za’a iya samun sakaci da makiyi zai iya samu domin ya kutsa kanshi har yayi ido biyu da shugaban kasa kuma ya cutar da shi cikin sauki,saboda rashin kwarewar jami’i wajen tantance take taken bako ko ma’aikacin gida ko kuma munafukin jami’in tsaro.

Matsawar za’a jagula tsarin ka’ida da gaskiya da tsari na son ra’ayi a wajen harkar kare lafiyar shuganni a Najeriya,akwai fargaban cewa karshen lamarin shine hakan zai iya haifar da mummunar sakamako da zai haifar da danasani ga wadanda abin ya shafa.

1.Daga karshe,ina ba mahukuntar Najeriya shawara akan cewa wajibi ne a bar jami’an DSS su tafiyar da aikin sun a tsaron lafiyar shugaba Buhari a matsayin jami’an kariya na zoben farko na tsaro.

2.Wajibi ne zobin tsaro na farko ya kasance jami’an DSS, sune masu bayar da jikin su domin dakile duk wani barazana da ido zai iya gani a matakin farko.

3.Zoben tsaro na biyu dole ne ya kasance jami’an na DSS saboda su ne masu yunkurin daukan mataki na gaggawa domin a janye shugaba daga wajen da aka fuskanci barazana zuwa wajen da ake zaton ya kasance tudun na tsira.Jami’ai ne da suke da horo na musamman akan matsayin su da kuma rawar da zasu taka a wajen tsaron lafiyar shugaban kasa,kuma sun sami horo daga hukumomin leken asiri na wasu manyan kasashen duniya da Amurka,Ingila da Isra’ila.

4.Zoben tsaro na uku shima DSS ne ya kamata ta rike,domin aikin wannan zoben shine samar da zaratan jami’an na DSS wanda aka basu horo na musamman kuma ake kira daya tamkar 20.Wadannan jami’an na DSS an basu wadataccen horo daga wasu hukumomin liken asiri na wasu kasashe kamar Musad na Isra’ila da hukumar leken asiri na Britaniya MI6 da kuma hukumar ayyukan asiri na Amurka (American Secret Service).Aikin wadannan jami’ai shine su mayar da wadataccen martini ga duk wanda ya tunkaro fadar da wata barazana musamman wanda ya shafi amfani da makami.

5.Wannan zoben shi ne ya shafi sauran jami’an tsaro da ake turawa fadar shugaban kasa ,amfanin su shine su bayar da Karin gudunmawa koda za’a fuskanci wata barazana.Wannan zoben shine ya kunshi jami’an NAIC,‘Yan sandan kwantar da tarzoma,Sojoji da jami’an Civil defence,FRSC da Fire service.

Daga karshe,kuskuren da aka samu shine duk wadannan ka’idodin an yi fatali dasu,sai ka gan jami’in day a kamata a zobe na biyar ya kutsa kanshi zuwa mataki na zobe na uku,wanda ke a matakin zobe na biyu an dawo da shi zuwa matakin zobe na hudu.Yanzu kai mai karatu,don Allah yaya zaka yanke hukunci a wannan tsari idan aka baka Alkalanci akan ko laifin waye ya sa aka bari aka sanya guba a bututun AC na dakin shugaban kasa?

Daga Isyaku Garba

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN