• Labaran yau

  Babban Dogarin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mutu

  Babban jami'in tsaron tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan watau Godwin Oduah ya mutu bayan yayi fama da mummunar ciwon zuciya a Asibitin tarayya dake Abuja.

  Hukumar DSS ta kama Godwin watanni kadan bayan uban gidanshi Goodluck Jonathan ya bar mulki inda hukumar ta tuhume shi da amfana da kudaden  ayyukan satan man fetur wanda ya musanta, dalilin da ya sa hukumar ta tsare shi a babban ofishinta da ke Abuja.

  Lamarin da ya sa Godwin ya shiga yajin kin cin abinci domin ya nuna rashin amincewarsa da ci gaba da tsare shi da hukumar tayi,lamarin da yasa lauyan sa ya janyo hankalin hukumar inda hukumar ta sake shi kuma daga bisani ya kamu da rashin lafiya.

  Hukumar ta nada wani kwamiti da yayi bincike akan lamarin Godwin da ya shafi amfana da kudaden harkar satar mai a yankin Niger Delta,amma kwamitin bai gamsu da jawabin da Godwin ya bayar ba kuma kwamitin ya bayar da shawar cewa a sallame shi daga aiki a hukumar ta DSS.A bisa wannan shawara ne hukumar ta DSS ta kori Godwin Oduah daga aiki kuma ta bukaci ya mika kayan aikin hukumar da ke hannunsa ga ofishin hukumar ba tare da bata lokaci ba.

  SHARHI

  Mutuwar Godwin Oduah ta wannan yanayi ba zai zama wani lamari na alhini ko tausayi ba ga yawancin jami'an hukumar ta DSS musamman 'yan Arewacin Najeriya idan aka tunada abinda wannan talikin yayiwa wasu 'yan Arewa a fadar shugaban kasa bayan shugaba 'Yar Adua ya rasu kuma Goodluck Jonathan ya zama shugaban kasa.

  Godwin Oduah yayi sanadin abin da ya faru dashi yanzu akan wasu jami'an ma'aikatar ta DSS shekarun baya a lokacin mulkin uban gidanshi Goodluck Jonathan musamman Musulmi 'yan Arewa da aka dinga yi masu bita da kulli bayan an koresu daga cikin jerin dogarawan tsaro ta DSS a fadar shugaban kasa a zamanin Goodluck Jonathan karkashin jagorancin Godwin Odua.

  Addini da lissafi na ilimi mai zurfi na tasrifi ya nuna cewa abinda kayi wa wani lallai za'ayi maka,kayi wa wasu ammaka amma ka sheka barzahu.

  Allah kasa mufi karfin zuciyarmu akan tsari na rashin adalci,Amin.

  Isyaku Garba

  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Babban Dogarin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mutu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });