Birnin Kebbi: Zanga zangar nuna rashin amincewa da Sanatoci

A yau Alhamis wata kungiyar matasa ta jagoranci wani zanga zangan lumana a cikin garin Birnin kebbi domin nuna adawa da abubuwan da ke gudana a Majalisar wakilai ta Najeriya musamman Majalisar Dattawa akan dambaruwar da take takun saka tsakanin 'yan majalisan Dattawan da fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Muhammad Bello Umar,wanda shine jagoran wannan zanga zanga,ya shaida wa manema labaru cewa amadadin hadin gwuiwar kungiyoyin matasa da kungiyoyi masu zaman kansu na jihar Kebbi suka tafiyar da zanga zangar.

A cikin wata takardar gayyata ga Al'umma wanda Muhammad Bello ya sanya wa hannu kungiyar ta ce "gayyata zuwa wajen zanga zangar lumana domin nuna bakin cikinmu da rashin amincewarmu akan yadda Sanatocin Najeriya ke wahalar da 'yan Najeriya da rashin baiwa mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari hadin kai da goyon baya domin cimma manufofi da cika alkawarin da akayi wa talakkawa a lokacin yakin neman zabe na 2015"

Zanga zangar wadda aka fara daga Masallacin idi dake unguwar Gesse ta biyo ta titin Ahmadu Bello kuma ta tsaya a fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu.Daga bisani masu zanga zangar sun bukaci su gan Mai Martaba  Sarkin Gwandu amma hakan bai yiwu ba.

Tawagar masu zanga zangar ta garzaya zuwa Gidan Gwamnatin jihar Kebbi,amma basu sami ganin Gwamna ba, Kwamishinan watsa labarai na jihar Kebbi Alh.A.C Ladan ya saurari koke daga masu zanga zangar kuma yayi masu alkawari cewa zai isar da sakon su ga mai girma Gwamna wanda yake hutawa bayan dawowa daga Kasar Saudiya inda ya gabatar da aikin Umra.

A yayin da ISYAKU.COM ya tuntubi wakilin Sanata Adamu Aliero Alhaji Abdullahi Zuru game da zarge zarge da masu zanga zangar suka yi musamman wanda ke rubuce a kwalaye game da Sanata Adamu Aliero,Abdullahi Zuru yace 'yan Najeriya na da 'yancin su fadi albarkacin bakin su ko ra'ayin su ta hanyar lumana.

Zuru ya kara da cewa ko miskala zarrati lamarin bai dame su ba ,yace" koda yake akwai rashin jituwa tsakanin majalisar Dattawa da Fadar shugaban kasa kuma 'yan Najeriya suna bayyana ra'ayin su a shafukan sada zumunta amma ina tabbatar maku da cewa Sanata Adamu Aleiru ba ranke ranken dan siyasa bane,ba dan tashi mu tafi bane,dattijo ne mai ra'yi ne na bauta ma jama'ar shi,ra'ayi ne na bauta wa kasa kuma mai ladabi da biyayya ga duk wanda Allah ya ba shugabanci a Najeriya."

Abdullahi Zuru ya ci gaba da karin bayani cewa,duk da wannan rashin jituwa da ake gani Sanata Adamu Aliero shine kan gaba wajen taimaka wa talakka domin dogaro da kansa da kuma bada taimako don tallafi ga talakkawa musamman na jihar Kebbi karashi ma 'yan mazabar Kebbi ta tsakiya.Ya kara da cewa ayyukan da Aliero yayi a Abuja lokacin da yake minista su ake takama da su haryanzu haka kuma a nan jihar Kebbi ayyukan da yayi a lokacin da yake Gwamna sune jihar Kebbi ke takama da su har yanzu saboda haka idan ana zanga zanga ne akan Sanatoci don rashin aiki ko cigaba to banda na mazabar Kebbi ta tsakiya.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb



Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN