Auren Islama a Kebbi: Ana ci gaba da tattaunawa akan shirin auratar da Zawarawa da Budare 100

A cigaba da tsarin tafiyar da harkokin shirye shiryen auren Islama a jihar Kebbi,dunkulalliyar kungiyoyi da sukayi hadaka domin tafiyar da wannan manufar sun gudanar da wani takaitaccen taro domin ci gaba da tuntuba a tsakanin su domin su tsara jaddawalin da zai zama turbar tafiyar.

A yayin da yake jawabi a wajen taron,Alh.Ibrahim Bayawa wanda kuma shine shugaban kungiyar taimakon marayu da zawarawa na jihar kebbi kuma jagoran wannan tafiyar ta auren Islama wanda yake wani sashe ne a karkashin kungiyar ta kula da marayu ya bayyana cewa aikin da kungiyar ta sa gaba aiki ne da zai samar da kwamitoci domin a tsara yadda tafiyar zai kasance a matakin farko.

Alh.Bayawa ya kara da cewa duk wani abu da aka fara a can baya za'a dakatar da shi a bisa wannan sabuwar hadaka da wasu kungiyoyi domin wadanda ba'a fara da su ba a can baya yanzu za'a sami damar farawa da su.

Kungiyar ta amince da rushe shirin na farko da wasu mutane suka zo da shi daga Sokoto da Kano game da lamarin auren zawarawa da budare a jihar Kebbi,kuma wannan tafiyar zai ta'allaka ne karkashin kungiyar taimaka wa Marayu wanda tuni yake tafiya akan tsari na doka da fahimta ta maudu'in ka'idar shirin.

Sakataren kungiyar Mal.Abubakar Sambawa ya karanto manufofin taron wanda aka yi mahawwara akai domin a sami mafita akan yadda tsarin tafiyar zai kasance.

Mal. Mainassara Sahabi Filin Sarki na mai Ahu daga Malam Sahabi Buwai jagora daga Darika ya samu halartar taron,wanda kuma ya albarkaci tattaunawar da irin nashi shawarwari.

Daga karshe,an rufe taro da addu'a bayan an sa ranar da za'a sake dawowa domin cigaba da tattaunawa.


Isyaku Garba

@ isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb


Y

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN