Kebbi: An kori Malami 1,an dakatar da Malamai 2 akan lalata da dalibai Mata

Gwamnatin jihar kebbi ta kori wani malami mai kula da jarabawa yayin da wasu malaman makarantar sakandare guda biyu suma aka dakatar dasu a kan laifin da ya shafi lalata da dalibai Mata na makarantun gaba da Sakandare.Kwamishinan ilimi na jihar Kebbi Muhammadu Aleiro ya shaida wa manema labarai haka a yayin da yake zantawa dasu a Sakatariyar Kungiyar 'yan Jarida na jihar Kebbi.

Aleiro yace Gwamnati ta dauki wannan matakin ne sakamakon rahotun da kwamitin da Gwamnati ta nada domin yayi bincike akan matsalolin.Ya kuma yi gargadi akan cewa duk wani Malami ko a Makarantar Gwamnati,ko a Makarantu masu zaman kansu da aka samu da laifi akan lalata da dalibai Mata za'a kore shi daga aiki,zai kuma iya fuskantar tuhuma a Kotu.

Kwamishinan ya kuma gargadi Dalibai Mata akan su daina soyayya ko wata ma'amala da Malaman su Maza matsawar ba harka ce da ta shafi karatu ba.Yace Dalibai Mata suna a Makarantu ne domin suyi karatu kawai.Aleiro yace kimanin yara 398,000 ne da shekarun su ya kai su shiga makaranta amma basa zuwa makaranta a jihar Kebbi.Yace Gwamnati tana kokari ta gani cewa ta cimma yarjejeniya ta Dakar akan yara da basa zuwa Makaranta.

Muhammadu Aleiro yace Gwamnatin jihar Kebbi ta kashe fiye da Naira Biliyan 1.6 wajen gyara da gina sababbin Makarantu domin a sami karin dalibai a makarantun Firamare da kananan Makarantun gaba da Firamare a jihar Kebbi.


@isyakuweb--Shafin mu na Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN