• Labaran yau

  Barnar amfanin gonar shinkafa,Uban kasar Aljannare ya koka

  An sami rudani a wani wuri da ake kira Chijoke a karamar hukumar mulki ta Suru da ke cikin jihar Kebbi a inda aka ce shanayen Filani Makiyaya sun yi wa amfanin gona mummunar barna a  gonar Hon.Dr Hussaini Kangiwa da Alh.Abu Hali.Wannan gonar dai rahoto yace noman rani ne aka yi a cikin shi inda aka shuka shinkafa,har ya zuwa lokacin da muka rubuta wannan rahotun bamu sami adadin girman gonar ba.

  A yayin da yake yi wa 'yan Jarida bayani,Uban kasar Aljannare Sarkin Sudan Aljannare Hon.Abubakar Saddik Dakin Gari ya bayyana barnar a zaman yi wa tattalin arzikin jihar Kebbi zagon kasa.Ya kara da cewa barnar da aka yi, ba abu ne da za'a iya yin misalin sa ba domin abin yayi munin gaske.

  Akwai jita-jitar cewa Filanin da ake zargi da aikata wannan aika-aika sun ce sun yi haka ne domin an shiga hurumin su. Rahoto ya nuna cewa Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya nada wani Kwamiti da zai bincika musabbabin wannan lamarin da kuma gano yadda za'a kiyaye irin wannan ibtila'i nan gaba.  Isyaku Garba  @isyakuweb  Ku biyo mu a Facebook
     • Facebook Comments
  Item Reviewed: Barnar amfanin gonar shinkafa,Uban kasar Aljannare ya koka Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });