Vision FM 92.9 B/Kebbi ta fara watsa shirye-shirye a garin Birnin kebbi

Vision FM 92.9 ta fara watsa shiye-shirye daga Equity Plaza da ke gabas da Asibitin Sir Yahaya gefen Ecobank a garin Birnin Kebbi.Tun ba yau ba dai ne ya kamata ace akwai fiye da gidan rediyon FM daya a babban birnin Jihar Kebbi.
Hakan zai haifar da ingantaccen ci gaba wajen ilmantarwa,fadakarwa,wayarwa da sanarwa ta hanyar sarrafaffen muryar radiyo sunfurin FM (freequency modulation) wanda taceccen tsarin murya ne mai inganci na zamani wanda ba iska a ciki.
Birnin kebbi na maraba da wannan tsarin wayewar zamani daga ma'abuta ci gaba da daidaita hakkin jama'a,domin Jihar Kebbi na fama da karancin mawallafa na kashin kan su ta yanar gizo watau "Bloggers" ko masu shafin yanargizo na kan su watau "website".Kacokan an dogara ne kan shafin sadar da zumunta na Twitter ko Facebook wanda ba kowa ne ke akan wannan tsarin ba kuma tsarin na dauke da nashi iyakan akan wallafi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN