Shugaban Jami'ar Maiduguri dake Arewaci Najeriya
Farfesa Abubakar Njodi ya ce rikicin kungiyar Boko Haram ya maida yankin
na Arewa maso gabashin Najeriya baya ta fannin ilmi da shekaru 500.
Farfesa
Njodi ya yi nuni da cewa tun kafin bullar kungiyar Boko Haram akwai
masana dake ganin an bar yankin a baya da kamar shekaru 150 ta fannin
ilmi bisa sauran sassan kasar musamman kudanci, sai gashi kuma an sami
wannan bala'i.Ya shaidawa tawagar komitin Asusun tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya cutar da suka ziyarce shi a Maiduguri, don jajanta masa sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai jami'ar da yayi sanadiyyar mutuwar ma'aikata uku, cewa ta fannin ilmi dai yankin na bukatar jama'a su mike sosai a tallafa.
RFI Hausa
Tags:
LABARI