Kamfanin Apple Ya Kaddamar Da Agogo Mai Aikin Likita

Kamfanin Apple ya kaddamar da wani agogo mai suna ‘Apple health watch’ wanda yake aiki iri daya da na likita domin kuwa mutane na iya dogara da agogon wajen tantance lafiyar su a kowane lokaci.
Agogon dai na dauke da wasu manhajoji da ke iya sanar da mutum idan akwai wasu cututtuka da ke kusantar jikin shi, don haka sai mutun ya dauki matakai da suka kamata. Haka kuma ya na iya sanar wa mutum irin yanayin halin da lafiyar shi ke ciki.
Agogon na amfani ne da ruwan zufar jikin mutun, da kuma yawan bugun zuciyar shi wajen tantance yanayin da lafiya ke ciki.
Masana a cibiyar binciken lafiyar dan’adam ta Jami’ar Stanford sun jaddada muhimanci amfani da wannan agogo, inda suka ce yana aiki kamar yadda likita ya ke yi, ko kuma kusanci da haka. Haka kuma masanan suna ci gaba da yin bincike akan iya aikin da agogon zai iya yi.
ALUMMATA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN