Illoli 8 Da Rashin Shan Isashshen Ruwa Ke haifarwa

Kowannen mu ya san muhimmancin da ruwa ke da shi wajen tabbatar da kasancewar mu cikin koshin lafiya, toh sai dai da yawa ba su san adadin ruwan da ya kamata su na sha ba.
Ko a tsakanin masana, babu daidaito a ra’ayoyin su game da wannan. Yayin da wasu ke ganin kofi 8 a rana ya wadatar, wasu suna ganin mutum na bukatar akalla lita 3 a rana.
Koma ya ya ne dai, jikin mutum kan yi masa nuni idan yana bukatar ruwa ta hanyar jin kishi, bushewar baki, jiri da sauransu. Kuma akwai matukar hatsari idan mutum ya ki la’akari da wadannan alamomi.
Akwai illoli da dama da rashin shan ruwa isasshe ke haifarwa, Kadan daga cikin su sun hada da:
1. Tamushewar fata da saurin tsufa
2. Rashin iya narka da abincin da aka ci da wahala wajen fitar da bahaya
3. Gyambon ciki
4. Rama
5. Ciwon gabobi
6. Zafin jiki
7. Mantuwa da toshewar kwakwalwa
8. Rashin kuzari da saurin gajiya
Da sauransu.
MUJALLARMU

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN