DOGARO DA KAI- KUNGIYAR MASU SAYAR DA WAYA A BABBAN KASUWAR BIRNIN KEBBI

Salisu Abubakar Warrah (Chairman)

Malam Salisu Abubakar Warrah shi ne chairman na kungiyar masu sayar da wayan salula a babban kasuwar Birnin kebbi  watau Birnin kebbi central market phone sellers association.
Ita wannan kungiyar ta masu sayar da wayar tana da rigista ne a mataki na karamar hukumar Birnin kebbi.Kungiyar dai tana cin gashin kan ta ne,ba tare da samun agaji ko tallafi daga kowa ba.Wadannan bayin Allah,sun rungumi wannan sana'a ne don samun biyan bukata da rufin asiri wajen tafiyar da rayuwar su.
Amma kungiyar na fuskantar matsaloli kama daga tsangwama na jami'an tsaro zuwa yaudara na masu sayar da wayoyin su ga 'yan kungiyar daga bisani kuma su zagaya su hada kai da abokan su a dawo wajen wanda aka saida ma wayar ace wayar sato ta aka yi.
Wannan ya zama wajibi a sami wakilci domin kalubalantar irin wadannan barazanar da sauran su.Shi dai Chairman Malam Salisu Warrah da sauran shugabannin kungiyar,sun sha zuwa har Bunza,Kalgo,Ambursa ko a nan cikin garin Birnin kebbi domin su sasanta matsala da ke tasowa game da 'yan kungiyar da bata gari da ke zuwa domin su yaudare su.
Anan,ina kira ga mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu a kan cewa ya taimaka wajen sa ido,da kuma ba da hankalin sa a kan abin da ke zuwa yana dawo wa kan harkar masu sayar da waya a babban kasuwar Birnin Kebbi,kuma a taimaka masu da tallafi da tsaro domin gudanar da sana'ar su.
Haka zalika,ina kira ga mai girma Chaiman na babban Kasuwar ta Birnin kebbi shi ma ya sa ido ta hanyar ba da taimako a wajen da taimako ya zama wajibi,musamman wajen barazana daga wajen wasu batagarin jami'an tsaro da ka iya amfani da matsayin su domi su muzguna ma jama'a.

SHARHI.
Yanzu haka akwai kungiyoyi na masu sayar da waya har guda uku zuwa hudu a cikin garin Birnin kebbi kuma kowace kungiya tana cin gashin kan ta ne ta hanyar fuskantar matsalolin 'yan kungiyar ta wai kowa ya san dakin uwar sa in ji masu iya magana.
Wannan ya samo asali tun lokacin da aka aka yi yunkurin kirkiro kungiya daya wanda zata wakilci duk wani mai sayar da waya a garin Birnin kebbi da murya daya,amma hakan bai yiwu ba a dalilai na son kai da kin gaskiya da wasu wadanda ke kallon kansu kamar su ne manya a cikin harkar sayar da waya a Birnin kebbi suka kirkiro tsari da ya haifar da rashin ragowa,muzgunawa wasu mutane,barazana,girman kai,raini da gina turban rashin mutunci,ba tare da nuna wani abin alkhairi zahiran ga jama'a ba face ace a rufe shagon wannan,ko an kori wancan daga wajen sana'a,ko an yanke hukunci a jahilce a kan abin da ba'a da wadataccen ilimi a tsarin sa,ko wani tsarin rashin basira irin na mutanen da suka yi rayuwa kukup a waje daya ba tare da marzaya wa cikin al'umma ba.
Daga bisani dai ya zama wajibi kowa ya kama gaban sa,shi ya sa aka sami kungiyar masu sayar da waya a gefen sakatariyar Haliru Abdu,da kungiyar masu sayar da waya a kasuwa,da kungiyar masu sayar da waya a Olumbo Plaza,Bello way,da 'yan gongonin waya,sai kuma 'yan ba ruwan mu wadanda suna sayar da wayar salular amma babu ruwan su da wata kungiya.
Zai zama babban kuskure ga ko wane mutum ya ce zai hukumta wani a kan zancen kungiya da ta karkata wajen rashi tsari da tafiyar da gaskiya,ga gazawa zahiran,kuma ga rashin kware wa a tafarkin tubalin tsara jaddawalin tafiyar tsari da ingancin kungiyanci mai ma'ana.

 


Wasanni - BBC Hausa

wasanni

Football (Sky Sports)

Sky Sports Football - Live games, scores, latest football news, transfers, results, fixtures and team news from the Premier to the Champions League.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN