Yanzu haka jami’an tsaro sun baza komar suna neman mamallakin gidan bulon da aka gano yaron ruwa a jallo.
Tun
misalin shekaru biyar ne da suka gabata iyayen wannan yaro mai shekaru
12 suka cire rai daga neman yaron nasu bayan ya bace, kuma an neme shi
an rasa.
An ceto yaron ne a wani gidan buga bulo
dake titin Oduduwa, yankin Ijapo na garin Akure bayan an ji muryarsa
yana taw aka cikin dare har na tsawon kwanaki uku.
Da
aka tuntubi iyayen yaron, sai suka ce wasu bokaye a baya sun fada musu
cewar matsafa ne suka yi amfani da yaron, don haka su daina bata
lokacinsu wajen neman shi. Jama’a da dama sun tausaya ma wannan yaron,
tare da al’ajabin yadda aka gine shi da kuma yadda ya rayu duk tsawon
shekarun nan.
Wani majiyar mu, wanda shima boka
ne ya bayyana mana cewar kiranye matsafa suka yi ma yaron, kuma ya
shafe shekaru 5 a cikin wannan hali, sa’annan suna ciyar dashi jinin
mutum da naman mutum daga duniyarsu irin ta matsafa.
Majiyar
namu ya shawarci iyayen yaron dasu mika shi ga hannun manyan bokaye don
su dawo da shi yadda ya kamata, saboda a yanzu haka sun canja shi.
Football (Sky Sports)
Sky Sports Football - Live games, scores, latest football news, transfers, results, fixtures and team news from the Premier to the Champions League.
Tags:
AL-AJABI