Yanzu-yanzu: Tinubu ya yi ganawar farko da kungiyar gwamnonin Najeriya


Shugaba Bola Tinubu yana ganawarsa ta farko da Gwamnonin Jihohi 36 na Tarayya da aka fi sani da Nigeria Governors’Forum (NGF) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

 An fara taron ne da misalin karfe 12:36 na rana. Jaridar The Nation ta rahoto.

 Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamnonin Zamfara, Kano, Taraba, Kogi, Ogun, Nasarawa, Bayelsa, Adamawa, Ebonyi, Lagos, Rivers, Osun, Jigawa, Benue, Taraba, Delta, Enugu, Rivers, Oyo, Plateau.  Kebbi, Abia, Imo, Bauchi

 Mataimakan gwamnonin Edo da Nijar ne ke wakiltar jihohinsu.

 Wadanda ba a gansu ba kafin fara taron sun hada da gwamnonin Katsina, Kaduna, Gombe, Borno, Cross River, Akwa Ibom, Anambra, Ekiti, Ondo da Sokoto.

 Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima;  Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume.

 Shugaba Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar sa ta APC mai mulki da aka fi sani da Progressive Governors’ Forum (PGF), a ranar Juma’ar da ta gabata.

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. MU DAI AL-UMMAR AREWACIN NIGERIA MUNA TUNWA SHUGABAN MU CEWA KADA MANTA ALFARMAR DA KAUNAR DA MUKA NUNAWA SHUGABA BOLA AHMED.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN