Saboda tsananin hidimtawa Buhari da nayi, sau 38 ana kulle ni – Buba Galadima


Shugaban tsagin sabuwar Jamiyyar APC mai lakabin rAPC Alhaji Buba Galadima, ya bayyana yadda abubuwa su ka same shi a dalilin shugaban kasa Muhammad Buhari.

Buba Galadima wanda tsohon makusancin shugaban kasa Buhari ne, ya bayyana cewa sau 38 ana garkame shi akan yana tare da Muhammadu Buhari, ya kara da cewa sau 5 ana yi masa tayin mukamin Minista amma yayi biris da tayin. Ya fadi hakan ne a lokacin da ya bakunci wani shiri da gidan talabijin na AIT yake a gabatarwa a kowacce Asabar. Sannan ya kuma ce yanzu wadanda su ke cikin gwamnatin shugaba Buhari yan ta fadi gasassa ne, domin 'yan ciranin siyasa ne. "Bani da wata matsala da Shugaba Buhari, domin kuwa tun daga watan janairun Shekarar 2002 na ke taimakonsa akan ya zama shugaban kasa. Domin na ba shi gudummawar da ko shi kan sa bai baiwa kansa ba, kuma babu wani dan kasar nan da zai iya wannann sadaukarwar" in ji Buba Galadima

Ya cigaba da cewa, "A dalilin shugaba Buhari na fuskanci tuhuma, dauri da kuma cin zarafi, kai har daure ni aka yi sau 38, amma hakan bai tsaya iya nan ba, domin kuwa har daure ne aka yi tamau tare da garkameni".

A karshe kuma ya bayyana takaicinsa dangane da yadda wasu mutane su ka kewaye shugaba Buhari, wadanda a baya su ne suke bayar da kudi domin ganin burinsa na mulkin kasar nan bai kai ga nasarar ba. Da ya ke bayani a kan dangantakarsu da shugaba Muhammad Buhari bayan an kammala zaben 2015, ya ce jim kadan da kaiwa ga nasarar zaben, sai shugaba Buhari ya yi taro da manema labarai na duniya, inda ya bayyana cewa ba shi da bukatar kuri'ata da ta magoya bayana da ta kuma iyalina da ma ta sauran duk wanda ya ke tare da ni. A karshe Buba Galadima ya tofa albarkacin bakin sa akan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin shugaba Buhari ta keyi, inda ya ce; "Wannan yana a matsayin wasa da Hankalin ne kawai, ya kamata gwamnati da ta sauya fasali da tsarin yadda ta ke yi akan yaki da cin hanci da rashawa"
 
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

hausa.naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN