Damar karshe: Bukatu 7 da R-APC suka gabatar gabanin ganawar su ta karshe da APC a yau


Gabanin wata ganawa ta karshe da shugabannin tsagin R-APC zasu yi da shugabancin APC a daren yau, Lahadi, jaridar Tribune ta wallafa wani rahoto dake kunshe da sakon 'yan tsagin na R-APC.

Rahoton ya bayyana cewar shugabannin R-APC din sun mika wasu bukatu 7 da suke burin shugaba Buhari ya cika masu a matsayin dama ta karshe da zasu bawa APC da gwamnatin Buhari kafin su fice cikin sati mai zuwa. Bangarorin biyu sun amince da yin wata ganawa da zata zama ta karshe a jerin ganawar yin sulhu da suke ta yi. Ga jerin bukatun kamar yadda jaridar ta Tribune ta rawaito; 

1. Tabbatar da dorewar Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattijai bayan zaben 2019. 

2. Tabbatar da Yakubu Dogara a matsayin shugaban majalisar wakilai bayan kammala zaben 2019.

3. Mayarwa da 'yan tsagin R-APC dukkan mukamansu da sabon zaben shugabannin APC ya tafi da su. 

4. A rushe zaben shugabannin jam'iyyar APC a jihohin da aka samu rabuwar kayuwa yayin zabukan shugabannin jam'iyyar. 

5. A sake yin zaben shugabannin jam'iyyar APC na kasa domin samar da shugabanci mai karfi.

6. Mayarwa da duk 'yan tsagin R-APC tikitin takara ba tare da wani sharadi ko zaben fitar da gwani ba. 

7. A janye dukkan wata kara da barazanar shiga kotu da 'yan tsagin R-APC. Wata majiya ta bayyana cewar wani wakilci daga ofishin shugaban kasa ya gana da Sanata Danjuma Goje tare da yi masa alkawarin cewar za a sassauta shari'ar da ake yi a kansa.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa .naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN