Za a yi bincike kan zargi da T.Y Danjuma ya yi wa sojin Najeriya - Buratai

Shugaban rundunar kasa na sojin Najeriya Lt. Gen Tukur Buratai ya kafa wani kwamiti wanda zai yi bincike a kan zargi da tsohon janar na soji T.Y Danjuma ya yi dangane da rikicin jihar Taraba.

A watan da ya gabata ne T.Y Danjuma ya zargi sojin Najeriya da aikata ba daidai ba a Taraba da Benue da kuma wasu sassa na Najeriya.

Danjuma ya zargi sojin Najeriya da mara wa masu kisan mutane baya a jihar Taraba tare da nuna goyon baya ga wani bangare a rikicin na Taraba.

Gen. Baratai ya ce wajibi ne a gudanar da bincike domin a tsabtace mutunci da darajar rundunar sojin Najeriya kuma bai kamata a yi fatali da irin wannan zargi ba.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Za a yi bincike kan zargi da T.Y Danjuma ya yi wa sojin Najeriya - Buratai Za a yi bincike kan zargi da T.Y Danjuma ya yi wa sojin Najeriya - Buratai Reviewed by on April 11, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.