Zargin satar kwalbar barasa 3 ya yi sanadin raunata Hausawa 6 a Edo

An sami wani tashin hankali tsakanin wasu matasa da yan kasuwa a kasuwar Ekiosa da ke Benin na jihar Edo a wani tashin hankali da ya yi sanadin raunata akalla mutum shida.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na ranar Laraba a magama na uku da ke cikin kasuwar da ke karamar hukumar Oredo a cikin jihar Edo.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan wani da ake kira Osaze ya zargi wani Bahaushe mai suna Abubakar cewa ya saci kwalba uku na barasa daga wani gidan giya zargi da Abubakar ya musanta nan take.

Punch metro ta ruwaito cewa duk da haka Osaze ya nace cewa Abubakar ne ya sace kwalba uku na barasa kuma ya yi barazanar cewa dole ne ya biya kudin barasan ko ya sha duka.

Ganin haka ya sa Hausawa da ke cikin kasuwar suka bukaci a yi hakuri domin zancen ya wuce amma matasan kabilu suka ki sakamakon haka matasan suka yi gangami domin su kai wa Hausawa farmaki.

Daga bisani yansanda daga ofishinsu na Esigie sun zo suka kori matasan, amma bayan yansandan sun tafi sai matasan suka afka wa Hausawan lamari da ya yi sanadin raunata akalla mutum shida.

Kwamishinan yansanda na jihar Edo Johnson Kokumo ya ce babu wanda ya rasa ransa kuma fada ne na cikin gari kuma an mayar da kwanciyar hankali.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN