Buhari ka mutunta kan ka kada ka tsaya takara a 2019 - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari cewa kada ya tsaya takaran zabe a shekara ta 2019. Obasanjo ya yi wannan jawabi ne a wata takarda da ya rubuta wanda ya yi wa taken 
THE WAY OUT: A CLARION CALL FOR COALITION FOR NIGERIA MOVEMENT

Obasanjo ya ce yanzu lokaci ne da shugaba Buhari zai nazarci gaskiya domin kada ya bata rawarsa da tsalle ta hanyar jarraba hakuri da jurewar 'yan Najeriya .Ya kara da cewa yanzu lokaci ne da ya kamata shugaba Buhari ya mayar da hankali kan neman hutawa a rayuwarsa ta hanyar mutunta kansa .
Tsohon shugaban kasar ya zargi shugaba Buhari da nuna bangaranci, ya kuma yi wa gwamnonin jam'iyar APC da suka je fadar shugaban kasa ranar 12 ga watan Janairu wankin mallen mashaya bisa neman shuga Buhari ya tsaya takaran zabe a 2019 musamman ganin cewa zuwan su fadar shugaban kasa ya zo ne awa 24 bayan kisan mutum 75 a jihar Benue.


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN