• Labaran yau


  Kwantena makare da makamai da kakin soja ya yi batan dabo

  Bayanai da suka fito daga tashar jiragen ruwa na Apapa da ke jihar Lagos ya nuna cewa wata kwantena mai tsawon kafa 14 makare da kakin soji da makamai ya yi batan daabo daga tashar ta jiragen ruwa.

  Vanguard ta ruwaito cewa kwamishinan 'yansanda da ke kula da tashar ta jiragen ruwa a Apapa CP Celestine Okoye ya bayar da umarni cewa wajibi ne a nemo wannan kwantena a duk inda aka kai shi.

  Haka zalika ya bayar da umarni a kamo wanda ya yi odar kayakin da wanda ya shigo da kayakin zuwa Najeriya, ya wa'adantar da awa 24 domin a kamo wadanda ke da hannu a cikin lamarin.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kwantena makare da makamai da kakin soja ya yi batan dabo Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama