Bakatafe ya Musulunta a babban Masallacin jihar Kebbi

Wani matashi mai suna David ya Musulunta yau a babban Masallacin jihar Kebbi watau Central Mosque da ke garin Birnin kebbi.

David wanda yanzu yake amsa suna Ibrahim ya shaida wa ISYAKU.COM cewa yanzu Mako biyu kenan yana mafarkin yana Sallah da duk wani abin da Musulmi suke yi, sakamakon haka ya gaya wa wani 'danuwansa wanda ya nuna masa cewa Musulunci ba addinin gaskiya bane.

Daga bisani 'danuwan nasa ya nuna masa cewa zai bashi duk abin da yake so domin ya fasa shiga Musulunci amma shi ya ki saboda abin yana damuwarsa.

David 'dan asalin Zangon kataf ne na jihar Kaduna ya ce mana ya yi imani da Allah cewa zai kare shi daga kowane irin barazana sakamakon cewa ya Musulunta.'Dan shekara 32 Ibrahim baya da Aure ya ce yanzu babban burinsa shine yadda zai yi karatu domin ya sami ilimin addinin Musulunci.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Bakatafe ya Musulunta a babban Masallacin jihar Kebbi Bakatafe ya Musulunta a babban Masallacin jihar Kebbi Reviewed by on November 10, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.