• Labaran yau

  Matashi ya gurfana a Kotu bisa zargin yi wa 'yar shekara 2 fyade a Gwandu

  Daga Isyaku Garba |

  A ranar Juma'a hukumar tsaron farin hula ta jihar Kebbi NSCDC ta gurfanar da wani matashi mai suna Yakubu Abubakar na unguwar Zoramawa bisa zargin yi wa wata karamar yarinya 'yar shekara biyu fyade a garin Gwandu da ke jihar Kebbi.

  Mai gabatar da kara Insp.Felix Ogbeke ya shaida wa Kotu cewa "Ranar 5 ga watan Nuwamba da misalin karfe 7:00 na yamma a unguwar Rummukawa Yakubu Abubakar ya yi wa yarinya 'yar shekara 2 mai suna Ummu Fyade yayin da ta je sayen dussan dabbobi a shagonsa.Felix Ogbeke ya ce hakan ya saba wa sashe na 283 na dokokin Penal Code na jihar Kebbi.

  Alkalin Kotun Majestare ta 5 Majestare Atiku Abubakar ya shaida wa mai gabatar da karan cewa Kotunsa bata da hurumin sauraron karan,sakamakon haka Majestare Atiku Abubakar ya bayar da umarni a tasa keyar wanda ake zargin zuwa gidan Kurkuku har zuwa lokacin da za'a sami shawara daga mai gabatar da kara na Gwamnati DPP.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Matashi ya gurfana a Kotu bisa zargin yi wa 'yar shekara 2 fyade a Gwandu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama