Ba za a tuhumi Mugabe ba bayan ya sauka daga mulki

Shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe ya sami tabbacin kariya bisa yarjejeniya da aka cin ma tsakaninsa da masu tafiyar da sulhu sakamakon juyin mulki da sojin kasar suka yi da farko wanda daga bisani ya zama mika mulki na ruwan sanyi ga mataimakin shugaban kasa da Robert Mugabe ya kora 'yan makonni da suka gabata wanda shi ne asalin ummul haba'is na rigimar.

Mugabe ya shaida wa masu shiga tsakani a yarjejeniyar cewa, yana fatan ya mutuwa ta riske shi a Zimbabwe kuma ba shi da burin rayuwa a kasar waje.

A ranar Talatar da ta gabata ne, Mugabe mai shekaru 93 ya sauka daga kujerar mulkin wanda ya dare tun a shekarar 1980 , lokacin da kasar ta samu ‘yanci daga Turawan Birtaniya.

Sojojin kasar sun taka rawa wajen kawo karshen mulkin Mugabe, yayin da jam’iyyarsa ta ZANU-PF ta juya ma sa baya.

Yanzu haka dai ana shirin rantsar da Emmerson Mnangagwa a gobe Jumma’a a matsayin shugaban kasar Zimbabwe na rikon kwarya bayan Mugabe ya sauke shi daga mukaminsa na mataimakin shugaban kasa sama da makwanni biyu da suka gabata.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Ba za a tuhumi Mugabe ba bayan ya sauka daga mulki Ba za a tuhumi Mugabe ba bayan ya sauka daga mulki Reviewed by on November 23, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.