Cutar kyandan biri ta yadu zuwa jihar Rivers da Akwa Ibom

An sami bullar cutar kyandan biri a jihar Akwa Ibom, wani babban jami'in Gwamnatin jihar yace akalla mutum 13 suna kwance a Asibiti a jihohin Bayelsa da Rivers da ke makwabtaka da jihar Akwa Ibom.

A wata sanarwa da ya fitar a Uyo, kwamishinan yada labarai na jihar Charles Udoh ya bayyana bullar cutar inda ake wa mutum daya magani yayin da Gwamnati ke ci gaba da bincike akan cutar.

Kwamishinan ya kara da cewa cutar ta kyandan biri yayi kama da cutar kyanda da aka saba da shi,yace banbancin cutar shine kuraje na kyandan biri sun fi girma bisa ga kurajen kyanda na asali.


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Cutar kyandan biri ta yadu zuwa jihar Rivers da Akwa Ibom Cutar kyandan biri ta yadu zuwa jihar Rivers da Akwa Ibom Reviewed by on October 09, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.