• Labaran yau

  Za'a gurfanar da wata Lauya a Kotu bisa zargin azabtar da 'yar shekara 9


  Elizabeth Agboje wata Lauya ce da ta fada hannun 'yansanda bisa zarginta da azabtar da yarinya da take riko mai shekara tara har tsawon shekara bakwai a garin Portharcourt na jihar Rivers.

  Binciken 'yansanda ya nuna cewa da farko dai an laka wa yarinyar Bright Maxson Maita, kafin a fara azabtar da ita.

  Yarinyar dai 'yar riko ce da ita Lauyan ta dauko ta hada ta da 'ya'yan ta na cikin ta su biyu.

  Kwamishinan 'yansanda na jihar Rivers Mr.Ahmed Zaki ya shaida wa manema labarai yayin da yake gabatar da wadanda ake tuhuma da aikata laifuka a jihar cewa rundunarsa zata gurfanar da Lauyan gaban kuliya bisa zargin azabtar da yarinya karama.

  Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Za'a gurfanar da wata Lauya a Kotu bisa zargin azabtar da 'yar shekara 9 Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama