Gulma da shan barasa ne kawai ake yi a cashewa na Bollywood - Sunny Doel

Sunny Deol wadda da ne ga fitaccen tsohon jarumin finafinan Bollywood Dhar Mendra Deol jarumi ne tsayayye kuma wadda baya daukan raini ko yin maula a tsarin tafiyar da rayuwarsa.

Sakamakon wannan salon rayuwa mutane da yawa da farko sun zaci cewa Sunny mutum ne mai girman  kai ko takama, amma daga bisani da dama sun fahimci tsarin rayuwarsa domin mutum ne da baya son shiga lamari da ba nashi ba kuma baya son yayi wani abu kawai wai domin ya burge wani matukar wannan abin bai yi daidai da abin da yake so ba.

Yayin da yake amsa tambaya daga wani dan jarida Doel ya shaida masa cewa shi baya son zuwa gayyatar cashewa watau Party da Bollywood ke shiryawa domin akasarin wannan cashewa ba abin da ke gudana a gurin bancin gulma da shan barasa da anyi-ance wadda bai yi daidai da tsarin rayuwarsa ba.


Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN