Yanzu haka jirgi na 4 dauke da alhazan jihar Kebbi ya baro Saudiya


Bayanai da ke fitowa daga Jidda na kasar Saudiyya ya nuna cewa yanzu haka jirgi na 4 dauke da Mahajjatan jihar Kebbi yana sararin samaniya akan hanyarsu ta dawowa jihar Kebbi .

Da misalin karfe 08:30 na Yammacin yau agogon kasar Saudiya rukunin Jirgi na 4 na  Alhazzan jihar Kebbi ya bar kasar saudiya zuwa Najeriya kuma Kamfanin Jirgin Sama na Max Air ne ya dauki Alhazzan jihar Kebbi zuwa filin Jirgin sama na Sir. Amadu Bello international Airport dake garin Birnin Kebbi inda jirgin ya dauki Mahajjatan jihar Kebbi kimanin 550.


Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Yanzu haka jirgi na 4 dauke da alhazan jihar Kebbi ya baro Saudiya Yanzu haka jirgi na 4 dauke da alhazan jihar Kebbi ya baro Saudiya Reviewed by on September 25, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.