Shugaban Kwamatin Sauka da tashin jirage na hukumar Alhazzan jihar Kebbi, Alh. Sani Dododo Birnin Kebbi ya bayyana cewa Alhazzan jihar Kebbi na jirgi na 3 sun isa a filin jirgin saman Sarki Abdul'Aziz dake Jidda.
Alh. Sani Dododo ya bayyana cewa da zarar Mahukuntan Saudiya sunka gama tantance Alhazai cikin ikon Allah Alhazan zasu tashi duk lokacin da aka gama tantancesu kuma Kamfanin jirgin sama na Max Air zai kwashesu zuwa filin jirgin Saman Sir. Amadu Bello international Airport dake Birnin Kebbi. Da fatar Mahajjatanmu zaku sauka gida lafiya.
Daga Ayuba Social Media
Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com