Ko ka san 'Liverpool za ta sayi Chamberlain' ?

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta tashi tsaye kan batun neman Oxlade-Chamberlain, wanda ake ganin ya fi son ya koma Chelsea, kamar yadda jaridar Sunday Mirror ta ruwaito.

Arsenal tana shirin sayen dan kwallon Real Madrid, Marco Asensio, a kan fam miliyan 75 gabanin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai ranar Alhamis, in ji jaridar Sunday Express.

Liverpool ta ba Barcelona wa'adin ranar Litinin kan ta fadi kudin da za ta sayi Philippe Coutinho, kamar yadda jaridar Onda Cero ta bayyana.

Everton tana zawarcin dan wasan Leicester City Jamie Vardy a kan fam miliyan 40, sai dai dan wasan ya son komawa Chelsea ne, a cewar jaridar Sunday Mirror.

Arsenal za ta sayar da Kieran Gibbs da Alex Oxlade-Chamberlain da Lucas Perez da Shkodran Mustafi kafin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai, kamar yadda jaridar Sunday Telegraph ta wallafa.
Kungiyar Juventus tana zawarcin dan wasan tsakiyar Barcelona, Andre Gomes, kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce bai fidda rai kan sayen Thomas Lemar daga Monaco da kuma Virgil van Dijk na Southampton ba, in ji jaridar Sun.

Paris St-Germain ta tashi tsaye kan zawarcin Kylian Mbappe a farashin fam miliyan 166 kafin ranar Alhamis, sai dai Monaco ta fi so ta sayar da dan kwallon ga Real Madrid, kamar yadda Sunday Telegraph ta ce


Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Daga shafin BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN