• Labaran yau

  August 31, 2017

  Amarya ta kashe jaririn uwargida bayan ta dura mashi pia-pia

  Rundunar yan sanda na jihar Bauchi ta kama wata mata Hindatu Abdullahi wadda ake tuhuma da kashe jaririn kishiyarta Fatima ta hanyar dura masa maganin kwari na pia pia lamarin da ya haddasa mutuwar jaririn mai suna Muhammadu.

  Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru a kauyen Wuro bogga a gundumar Duguri na karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauch.Majiyarmu ta shaida mana cewa Hindata wadda ita ce Amarya ta shiga dakin Fatima wadda ita ce uwar gida bayan Fatima ta tafi gidan makwabta sai Hindatu ta dauki jaririn Fatima ta kaishi dakinta inda ta dura mashi pia pia.

  Daga bisani Fatima ta dawo ta tarar da lamarin da ya auki wadda a bisa wannan daliline ta nemi agaji.Daga bisani an garzaya Asibiti da jaririn inda aka tabbatar da rasuwarsa.

  Hindatu dai ta fada hannunu yan sanda yayin da shi maigidansu Mal Abdullhi yana Saudiya wajen aikin Hajji.
  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Amarya ta kashe jaririn uwargida bayan ta dura mashi pia-pia Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama