• Labaran yau

  July 28, 2017

  Yara 'yan aji 6 a firamare ba su iya karatun fatiha ba.

  Yara 'yan Aji 6 a firamare ba su iya karatun fatiha ba .Wannan ya faru ne a wata makaramta a wani Kauye da ake Kira "Sakace" a karamar hukumar Mulki ta shanga. 

  A lokacin da na shiga aji shidda domin tabbatar da wannan, na nemi  wasu daliban su karanta mini wani abu a cikin Qur'ani sai suka kasa !

  Daga nan ne na nemi su karanta mini  "suratul fatiha"  wallahi ban samu yaro ko daya da ya iya karantawa ba !
  Wannan yasa na kalubalanci Malamin da yake koyar da wannan darasin cewa ya akayi hakan ya faru ?

  Yace shima baijima da zuwa ba haka ya tarar da su , kuma yana iya kokarinsa akan wannan matsalar.
  To abin tambaya anan shine:

  Ya akayi yaro zai kai aji shidda amma bai iya fatiha  ba ?

  Laifin waye a cikin wadannan ? 

  1  Gwamnati

  2  Iyaye,

  3  Shugaban Makaranta (Head Master) 

  4  Malaman Makaranta


  Daga Sani Musa Saminaka
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yara 'yan aji 6 a firamare ba su iya karatun fatiha ba. Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama