• Labaran yau

  July 12, 2017

  Shugaba Buhari ya sami sauki sosai,zai dawo ba da dadewa ba- Osinbajo | isyaku.com

  Mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo ya ce shuga Muhammadu Buhari yana murmurewa kuma sauki ya bayyana sosai a jikinsa.

  Osinbajo ya shaida wa manema labarai haka a Fadar shugaban kasa a yau gabanin taron zartarwa na kasa a Abuja.

  Yayin da yake bayani dangane da ziyara da ya kai don ganin shugaba Buhari,Osinbajo ya ce " Na tafi domin na ganshi da ido kuma na gaida shi,kuma nayi masa bayani yadda ababe ke tafiya a kasa domin ko dama can ai ina magana da shi a koda yaushe amma naga magana ta wayar tarho kadai bai wadatar ba shi yasa na je na gan shi".

  "Yana cikin yanayi mai kyau kuma nan ba da dadewa ba zai dawo Najeriya" inji Osinbajo.

  Kalli bidiyo a kasa.
     Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Shugaba Buhari ya sami sauki sosai,zai dawo ba da dadewa ba- Osinbajo | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama