An damke jami'an Banki 3 da suka sace N150m na kostoma | isyaku.com

Yansanda a jihar Lagos sun damke wasu ma'aikatan Banki su uku da wasu mutum uku a bisa zargin satar kudin kostomomin Bankin da ya kai fiye da N150m.

Jami'an Bankin da aka kama sun hada da Oyelade Shola-Isaac, 32, Osuolale Hammid, 40, sai Akeem Adesina, 33.

Sauran mutanen da aka kama da zargin taimakawa domin a aikata zamban sun hada da Okpetu John, 29; Chukwumnoso Ifeanyi, 30 da Salako Abdulsalam wadanda ake zargin cewa jami'an kamfanin sadarwa ta MTN ne sai Ismaeel Salami, 49; Akinola Oghuan, 34; Sarumi Abubakar, 32; James Idagu, 56; da kuma dan shekara 33-Sunday Okeke.

Punch Metro ta ruwaito cewa jami'an hukumar yansanda sashen kula da ayyukan zamba sune suka damke jagoran kungiyar Salami wanda hakan ya kai ga kamo sauran wadanda suke da hannu a cikin wannan badakalar cin amana.

Rahotanni sun nuna cewa jami'an Bankin sukan zuki yan kudade ne daga asusun ajiya na kostoma wadanda basu da tsarin sanarwar hulda ta ma'amala da Banki wanda ake kira alert saboda haka koda sun karkatar da yan kudade kalilan kostoma bazai iya ganewa ba kuma da yake akin ya shafi  asusun ajiya na mutane da yawa wanda jimilar ya kai har fiye da Naira miliyan dari da hamsin wanda ake zargin jami'an sun wawure.

Yansanda a garin Lagos suna ci gaba da bincike.





Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN