Me ya bambanta rashin lafiyar Buhari da ta 'Yar Adua?

Fiye da wata biyu ke nan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake jinya a kasar Birtaniya, hakan ya sa wasu 'yan kasar fara fargabar ko doguwar jinyar tana kama da wadda tsohon Shugaban Najeriya Umaru Musa 'Yar adua ya yi gabanin rasuwarsa a shekarar 2010.

Shugaba Buhari ya fara tafiya kasar Birtaniya domin "hutun jinya" a ranar 9 ga watan Janairun bana inda daga bisani ya bukaci masalisar dokokin kasar ta kara masa tsawon hutun jinyan.

Ya koma gida Najeriya a watan Maris, amma sai dai ya sake komawa Landan ran 7 ga watan Mayun da ya gabata wanda har yanzu yake can yana jinya.

Hakan ya sa wasu 'yan kasar fara fargabar kan ko tarihi ya fara maimaita kansa ne?

Me ya sa ake ganin doguwar jinyar Buhari tana kama da ta marigayi 'Yar Adua? 

Masu sharhi a kasar suna danganta abubuwan da suka faru lokacin doguwar jinyar tsohon Shugaban Najeriya marigayi Umaru Musa 'Yar Adua da wadanda suke faruwa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaba Yar'adua ya rasu ne a watan Mayun shekarar 2010 bayan ya yi doguwar jinya.

"Rashin lafiyar Buhari yana kama da na 'Yar Adua ta fuskar yadda ake boye ainiyin halin da yake ciki ga al'ummar kasar," in ji Malam Kabiru Danladi Lawanti na Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya.

Duka shugabanin sun fito ne daga arewacin kasar kuma daga jiha guda wato Katsina. Haka zalika dukansu Fulani ne.

Ga batun yadda shugabannin suka bazama kasashen ketare neman magani, maimakon su tsaya a gida.
Sai dai bambancin shi ne 'Yar Adua ya yi jinya ne a wani asibiti da ke birnin Jeddah na kasar Saudiyya, yayin da Buhari yake jinya a gidan gwamnatin kasar da ke birnin Landan na kasar Birtaniya.

Wane ne ke tafiyar da kasar?

Tun lokacin jinyarsa ta farko a watan Janairu, Shugaba Buhari ya mika ragamar tafiyar da kasar a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, inda yake jagorantar kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

An yi zaton cewa bayan dawowarsa jinya a watan Maris din da ya wuce zai karbi ragamar tafiyar da kasar nan take, amma sai shugaban ya ci gaba da "hutawa a gida."

Abin da ya sa wasu suke cewa tarihi ne ya maimaita kansa.

Inda ake kwatanta hakan da lokacin da aka dawo da 'Yar Adua jinya daga Saudiyya a watan Fabrairun shekarar 2010, inda ya ci gaba da jinya ne a fadar shugaban kasa amma shi ma bai ci gaba da tafiyar da aikinsa na shugaban kasa ba

Kamar yadda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rike ragamar kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa yayin jinyar marigayi 'Yar Adua, haka Mista Osinbajo yake tafiyar da kasar a yanzu.

Sai dai dan bambancin shi ne majalisa ce ta nada Mista Jonathan matsayin, yayin da Osinbajo kuma Buhari ne da kansa ya aike da bukatar hakan ga majalisar dokokin kasar kafin ya bar kasar.

Jonathan da Osinbajo duka sun fito ne daga kudancin kasar.

Sai dai gwamnatin Buhari ta kaucewa takaddamar da kasar ta

 fada ciki kan wanda zai tafiyar da kasar lokacin jinyar 'Yar Adua wadda har sai da majalisa ta fitar da mafita.
Hakan bai rasa alaka da yadda Buhari ya bai wa mataimakinsa Osinbajo damar zartar da manyan al'amura ciki har da sanya hannu a kasafin kudin kasar na bana.

Ciwon da Buhari yake fama da shi

Har yanzu dai ba a bayyana cutar da ke damun Shugaba Buhari ba.

Sai dai game da tsohon Shugaba 'Yar Adua an bayyana cewa ciwon zuciya ne ya yi fama da shi.

Har ila yau, marigayi Shugaba 'Yar Adua ya kasance yana da tsohon tarihin fama da rashin lafiya tun lokacin da yake gwamnan jihar Katsina wato tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007.

Ko da yake, Shugaba Buhari ba shi da tarihin fama da wani babban ciwo, amma bayan dawowarsa jinyarsa ta farko a bana ya ce bai taba yin rashin lafiya a rayuwarsa kamar wadda ya yi ba a lokacin.

Akwai bambancin shekaru tsakanin 'Yar Adua wanda ya rasu yana da shekara 58, yayin da a bana Buhari yake cika shekara 74 a duniya.

Rashin bayyana a bainar jama'a

'Yan kasar suna ci gaba da bayyana damuwarsu kan yadda shugaban ya ki bayyana a bainar jama'a, wanda hakan ma yake kama da abin da ya faru lokacin jinyar marigayi Shugaba 'Yar Adua.

Dalilin haka ne ya sa wasu suke ganin bai dace a ci gaba da yin rufa-rufa ba game da halin da shugaban yake ciki.

Ko da yake, akwai masu ganin cewa sakon muryar da Shugaba Buhari ya aike wa 'yan kasar yayin bikin karamar sallah ya wadatar, wanda hakan ya yi kama da wanda 'Yar Adua ya aike wa 'yan kasar lokacin yana kan gadon jinya.


Tun bayan da Buhari fara jinya ne wasu 'yan siyasa a kasar musamman 'yan jam'iyyar PDP suka fara cewa ya kamata shugaban ya yi murabus.

Gaba-gaba wajen wannan kiran shi ne Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose, wanda ko a ranar Larabar da ta gabata ma sai da gwamnan ya sake cewa "lokaci ya yi da Buhari zai yi murabus".

Ko da yake, wannan ba sabon abu ba ne don ko lokacin jinyar 'Yar Adua an sha yin irin wannan kiraye-kirayen, ciki kuwa har da shi kansa Shugaba Buharin inda ya yi kira ga majalisar kasar da ta sauke shi "don shugaban ba zai iya jan ragamar kasar ba."

Hana Buhari ganawa da jama'a

Kamar yadda na kusa da marigayi 'Yar Adua suka hana kowa ya je kusa da shi bayan wasu kalilan, akwai masu zargin cewa hakan yana faruwa yanzu da Buhari yake jinya.

Buhari ya gana da mataimakinsa Osinbajo a ranar Talata, sabanin yadda aka hana Mista Jonathan ganawa da 'Yar Adua har sai bayan da ya koma ga Allah.

Yaushe Buhari zai dawo?

Wannan tambaya ce da 'yan Najeriya suke yawan yi.

Sai dai kawo yanzu babu tabbas kan lokacin da shugaban zai koma gida Najeriya.

An sha ruwaito uwargidansa Aisha da mataimakinsa Osinbajo suna cewa shugaban yana samun sauki kuma ya kusa dawowa.

Ko a lokacin da tsohon Shugaba 'Yar Adua ya kwashe lokaci mai tsawo na jinya an ta cewa shugaban ya kusa dawowa, sai dai ya koma gida ne cikin dare amma gwamnatinsa ba ta sanar da kowar ba.



 Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Daga BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN