Ma'aikatar cinkin gida ta daidaita albashin masu HND dadai da na masu DEGREE

Ma'aikatar cikin gida na Najeriya ta daidaita matakin albashi na masu amfani da takardar karatu na HND zuwa daidai da na masu DEGREE.

Wannan ya biyo bayan wani taro na zartarwa da Ministan ma'aikatar cikin gida Lt Gen. Abdulrahman Dambazau ya jagoranta ranar Talata da ya gabata inda ya amince da kudurin.

Sakataren dindindim na ma'aikatar cikin gida Abubakar Magaji ya fitar da sanarwa cewa daga yanzu masu takardar karatu na HND zasu fito a matsayi na babban safeto (Cheif Inspector),yayin da masu DEGREE zasu fito a matsayin mataimakin supritanda (Assistant Supritendant).

Sanarwar ta bayyana cewa an umarci dukkannin ma'aikatu da ke karkashin ma'aikatar cikin gida su daga albashin masu HND zuwa mataki na COMPASS 08 daidai kenan  da na masu DEGREE.

Ma'aikatar cikin gida ta kunshi ma'aikatu kamar Customs,Immigration,Prisons,FRSC,NSCDC da sauransu.

Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN