• Labaran yau

  July 19, 2017

  Kamfanin Jamus ya roki Osinbajo ya sa baki Zamfara ta biya su kudin kwangila

  Kamfanin kasar Jamus da ke aiki a jihar Zamfara Connexx Plants Ltd.ya raki Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo domin ya sanya baki Gwamnatin jihar Zamfara ta biya su ragowar kudin kwangila da ta kammala wa Gwamnatin ta jihar Zamfara wanda adadin kudin ya kai Naira Miliyan 195.

  Babban Manajan kamfanin Connexx Mr.Richard Klosa ya shaida wa manema labarai haka a Abuja ranar Talata yayin taron manema labarai.

  "Yace kwangilar ya shafi kayaki da na'urorin sadarwa da kamfanin ya sayo wa gidajen rediyo na jihar Zamfara a 2013."

  Klosa ya roki Mataimakin shugaban kasa,Majalisar wakilai ta kasa,Ma'aikatar sharai'a ta Najeriya,Jami'an tsaro da sauran Manyan mutanen kirki a Najeriya da su taimaka don ganin cewa Gwamnatin Zamfara ta biya Kamfanin kudinta.


  Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb = Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.= Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. = Shiga shafinmu kai tsaye www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kamfanin Jamus ya roki Osinbajo ya sa baki Zamfara ta biya su kudin kwangila Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama