An sami karin tashin bamabamai a Maiduguri

An sami jerin tashin wasu bamabamai a birnin Maiduguri a ranar Talata da misalin karfe 10:30 zuwa 11:00 na dare lamarin da ya faru awa 12 bayan an sami tashin bam sakamakon kunar bakin wake da ya halaka mutun 12 har da 'yar kunar bakin waken.

Rahotanni sun nuna cewa fashewar ya haddasa girgizan kwanon rufin gidaje wanda ya haifar da fargaba sakamakon tsananin karfin fashewar.

An ji karar fashewar har sau biyar,karar wannan fashewar ya bambanta da sauran karar fashe fashen bamabamai da aka saba ji a baya inji kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN.

Sanadi da yanayin wannan hari yana da sarkakiya kafin wannan lokaci da muka rubuta wannan labari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN