• Labaran yau

  July 10, 2017

  Illela Yari B-kebbi: Fiye da shekara 150 Makerar Jadda na nan da martabar ta | isyaku.com

  Malam Muhammed Shehu wani Makeri ne wanda ya shafe shekara arba'in da hudu yana sana'ar kira a Makerar Jadda wanda sanannen Makera ne a unguwar Illela Yari da ke garin Birnin kebbi.Malam Muhammad ya shaida mana cewa shidai a sana'ar kira saidai suce Alhamdu lillahi saboda kwalliya ta biya kudin sabulu.

  A ci gaba da hira da ISYAKU.COM Mal. Muhammad ya shaida mana cewa suna da yawa a cikin gidan nasu wanda ya hada da jikoki,'ya'ya ,uwaye da kakanni da sauransu wanda suka gaji sana'ar daga kakansu kuma suka rike sana'ar har yanzu.

  Makerar Jadda Makera ce da ta kafu fiye da shekara 150,kuma har yanzu tasiri da ingancinta yana nan daram inda ake ci gaba da gudanar da aikin sana'ar kira har yanzu a wajen.

  wannan Makera ta shahara a wajen kirar farin karfe,azurfa ,zinari da sauransu.Wasu ababe da ke gagara a tsarin zamani akan kawo masu su gyara kamar almakashin aikin Asibiti,da na'urar duba kunne na Likitocin kunne da sauransu.

  Mal.Muhammada ya shaida mana cewa har yanzu dai babu wani tallafi ko taimako da Makerar Jadda ta taba samu daga Gwamnati ko na jiha ko na tarayya ko kuma taimako daga wani mai hannu da shuni duk da yake Makerar na taimakawa wajen samar da sana'ar yi ga yara da Matasa a cikin garin Birnin kebbi.

  Makerin yayi kira ga Gwamnatin jihar Kebbi karkashin Gwamnatin Alh.Atiku Bagudu ta kawo masu dauki ta hanyar samar da isassun kayan aiki wanda samar dasu zai inganta sana'ar tasu sakamakon haka za'a sami ci gaba da bunkasar arziki a cikin al'umma.

  Daga karshe Mal.Muhammad ya yi kira ga Matasa akan cewa su zo su koyi sana'ar kira domin basa karban ko kwabo kafin yaro ya fara koyon sana'ar,yayi harsashen cewa idan matasa sun koyi sana'a hakan zai taimaka wajen rage matsalar shaye shaye da sace sace a cikin al'umma musamman tsakanin Matasa.


  Daga Isyaku Garba- Birnin kebbi
  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Illela Yari B-kebbi: Fiye da shekara 150 Makerar Jadda na nan da martabar ta | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama