Osinbajo ya sanya hannu a kasafin kudin 2017 amadadin shugaba Buhari | isyaku.com

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, ta ce shugaba Buhari ya ba mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo damar sanya hannu a kan kasafin shekara ta 2017.

Tuni dai mmukaddashin shugaban kasar ya rattaba wa kasafin hannu da misalin karfe 5 na yammacin Litinin din nan.

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Malam Garba Shehu, ya ce shugaban Buhari ya ba farfesa Yemi Osinbajo damar ne bayan an ba shi cikakkun bayanai a kan abin kasafin ya kunsa.

Nijeriya dai ta na son ta kashe sama da naira triliyan 7 a kasafin bana, yayin da ta ke fama da karayar tattalin arzikin da ta dade ba ta samu irin sa ba.@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com


Daga  shafin Liberty
Osinbajo ya sanya hannu a kasafin kudin 2017 amadadin shugaba Buhari | isyaku.com Osinbajo ya sanya hannu a kasafin kudin 2017 amadadin shugaba Buhari | isyaku.com Reviewed by on June 12, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.