PDP a Jihar Kebbi Zata kalubalanci Hukumar zabe da Jamiyyar APC a Kotu | isyaku.com

Hakan yasa jamiyyar ta PDP zargin hada bakin hukumar zaben da jamiyyar APC mai mulki domin hana su shiga zaben.

Umar Na Amore shine dan takarar shugabancin karamar hukumar mulki ta Argungu karkashin inuwar jamiyyar ta PDP, ga kuma korafin da yayi a hira da wakilin sashen Hausa Murtala Faruk Sanyinna yayi da shi.

‘’Ance mu kai takardun mu na ‘yan takara, mun kai a ranar 27, lokacin da ita shugaban hukumar zaben ya kira shugaban jamiyya cewa an kara wa’adin lokacin gudanar da zaben da sati guda bisa lokacin da suka sa na karban sunayen ‘yan takarar da za’a yi zaben da su. Bayan mun kai, an karba. Daga baya hukumar zabe ta kira shugabannin mu cewa suzo su karbi sunayen akan cewa mun wuce lokacin da aka ce a karbi takardun mu. Lokacin da aka ce an kara wa sati guda, ya kai kafin wannan lokacin ake cewa ya wuce?.
Sai dai hukumar zaben ta jihar Kebbi ta musunta wadannan zarge-zargen, kamar yadda shugabanta Aliyu Mohammed Mera ke cewa.

‘’Kasan Al’amurran mutane ko baka wa kanka adalci ba sai kayi kokari ka aza ma wani. Abinda aka ce shine za rufe a ranar 26 ga wata, baka kawo ba sai 2 ga wata na wani watan da ya shigo,lokacin ka kawo to yanzu wanene baiyi adalci ba?.@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

Daga shafin VOA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN