• Labaran yau

  June 01, 2017

  Dalilin da ya sa kudin aikin Hajjin bana yayi tsada | isyaku.com

  Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta bayyana dalilan da suka sa aka samu karin kusan kashi 50 bisa dari a kudin kujerar aikin hajjin bana a kasar. 

  A makon nan ne hukumar ta bayyana yawan kudaden kujera a bana wanda ya nuna kudin kujera mafi karanci shi ne sama da Naira miliyan daya da rabi.

  Hakan dai ya sa wasu maniyyata da dama a Nigeria yanke kaunar sauke faralin a bana.
  To sai dai shugaban hukumar Alhaji Abdullahi Mukhtar Muhammad ya ce, karin ya tsaya a kashi hamsin bisa darin ne ma saboda rangwamen da gwamnatin kasar ta yi wajen yi wa maniyyatan canjin dalar Amurka.

  Alhaji Abdullahi Mukhtar Muhammad ya kara da cewa, faduwar darajar Naira shi ne ginshiki na karuwar farashi, duk kuwa da rangwamen da gwamnatin kasar ta yi.

  Shugaban hukumar aikin Hajji ta Najeriyar ya kara da cewa a wannan karo an samu raguwar Dala dari uku a kudin da alhazai ke biya na masauki da kuma kudin jirgi.

  A bara dai maniyyata daga arewacin kasar sun biya Naira 998,248.92 a karamar kujera, wasu kuma sun biya Naira 1,047,498.92 na matsakaiciyar kujera, kana masu babbar kujera sun biya Naira 1,145,998.92.
  Su kuma maniyyata daga kudancin kasar sun biya Naira 1,008,197.42, su kuma masu matsaikaiciyyar kujera kuma sun biya N1,057,447.42, inda masu babbar kujera suka biya Naira 1,155,947.42.

  A bana an soke wannan tsarin kujeru daki-daki, inda aka mayar da shi na bai daya, kuma kowane maniyyaci zai biya abin da jiharsa ta kayyade.

  A bana an tsayar da guzurin bai daya na dala 800 na Amurka.
  Ga jadawalin kudaden da maniyyata daga Najeriya za su biya:

  Nasarawa:1,544,894.16
  Niger:1,525,483.30
  Kaduna:1,535,503.68
  Kano:1,537,859.97
  Katsina: 1,498,502.70
  Adamawa:1,530,101.18
  Yobe:1,520,101.18
  Kano:1,537,859.97
  FCT:1,538,218.62
  Bauchi:1,523,122.41
  Plateau:1,529,036.80
  Zamfara:1,510,461.65
  Sokoto:1,524,618.90
  Gombe:1,516,118.90
  Benue:1,522,118.90
  Kebbi:1,534,659.85
  Taraba:1,521,138.21
  Osun:1,548,153.42
  Armed Forces:1,538,379.22
  Ogun:1,561,943.97
  Anambra:1,511,173.77
  Kwara:1,501,571.27
  Ekiti:1,525,191.27
  Edo:1,551,331.87.
  Oyo:1,584,069.02.

  Ban da wadannan kudaden, akwai Naira 38,000 na hadaya da kowane maniyyaci zai biya daga aljihunsa a Makkah.  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com


  Wannan labarin ya fara baiyana a shafin BBC
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dalilin da ya sa kudin aikin Hajjin bana yayi tsada | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama