NSCDC ta kori jami'in ta kan cin zarafi | isyaku.com

Rundunar jami'an tsaro na NSCD a jihar Bayelsa ta kammala bincike akan wasu jami'anta su biyu ba yan an zarge su da cin zarafin wani Likita Bekewari Sampou kuma suka harbi motarsa da bindiga a Yenagoa na jihar Bayelsa.

Lamarin ya faru ne a ranar 28 ga watan Afrilu wanda ya shafi jami'an hukumar su biyu Akpoghomhe Jude da Ogodo Richman.Aukuwar lamarin ya janyo cece-kuce a cikin al'umma musamman kan yadda ake samun rahotun karuwar zargin cin zarafin jama'a da jami'an hukumar ke yi.

A bisa wannan dalilin ne rundunar ta jihar Bayalsa ta nada wani kwamitin bincike na mutum 7 karkashin mataimakin kwamanda sashen bincike na hukumar D.C Anyanwu,wanda bayan aiwatar da bincike ya sami jami'in da laifi.

Kwamandan rundunar na jihar Bayelsa Mr.Desmond Agwu yace bayan kammala bincike hukumar ta sami Jude Akpogho da laifi kuma hukumar ta dakatar da shi daga aiki nan take,ya kuma kara da cewa hukumar ba zata lamunta da rashin da'a da cin zarafin al'umma ba da ga jami'an hukumar NSCDC musamman wajen yin amfani da makami ta hanyar da bai kamata ba.

Rahotu daga wata majiya kuma ya nuna cewa hukumar ta yi sulhu da Likita da abin ya shafa inda aka biya shi diyya bayan kungiyar Likitoci ta Najeriya ta shiga tsakani.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN